Yadda Zaki Matse Gabanki Ya Koma Tamkar Wani Bai Taba Haduwa Dake Ba

Yadda Zaki Matse Gabanki Ya Koma Tamkar Wani Bai Taba Saduwa Dake Ba

Mata da yawa suna Fama da wannan Matsalar ta Buɗewar gaba, wasu In sun Haihu Wasu kuma In suna Hawa Keke me taya biyu, wasu kuma In suna Tsalle-tsalle, wasu kuma In Anyi Musu Fyaɗe.

Idan kina Buƙatar Gaban ki ya tsuke Ya dawo kamar na Yarinyar wacce batasan ɗa Namiji ba a rayuwar ta to ga Matakan da Zaki bi:

Na Daya :

-Bagaruwar Hausa

-Ganyen Magarya.

Idan kika samu waɗannan abubuwa sai ki dafa su, ko kuma ki dafa ita bagaruwar ita kaɗai, sai ki rinƙa wanke gabanki da ruwan, ko ki zuba a baho ki zauna a ciki da ɗumi ɗumin sa kaman minti talatin (30)mints a ƙalla sau biyu a sati.

Na biyu:

2- Kanunfari.

Zuma (Pure Zuma).

In kika same su Se ki dafa da zuma, ki rinƙa shan sa da zafin sa, ko ki jiƙa shi ya kwana da safe ki tace kisha da madara da zuma.

Na uku:

3-Kanunfari.

Ana kuma dafa shi kanumfarin a zauna a ciki da ɗumi-ɗumin sa ko a riƙa tsarki da ruwan ko kuma a zuba kanun fari a garwashi a tsugunna, ayi turare, shi ma sau 2 a sati

Na Hudu:

4-Kwallon mangwaro.

Zuma (Me kyau).

Idan kika samu kwallon Mangwaro seki fasa shi, zaki ga ɗan cikin fari, sai ki shanya shi ya bushe, to Idan ya bushe sai ki daka shi, a kwaba da zuma sai ki rinƙa sa shi a gaban ki da daddare bayan isha’I, amma idan zaki kwanta bacci sai ki wanke Gaban naki.

Na biyar:

5-ko kuma ki dafa ɗan cikin da bagaruwa, ki wuni kina tsarki dashi, ko ki zuba ruwan a baho sai ki riƙa zaunawa a ciki shima a ƙalla sau uku a sati.

Na Shida:

6-Bagaruwar Hausa.

Chikui (Dabino).

Inkika samu Bagarauwa sai ki Shanya ta ta bushe, Sai ki dakata ki tankaɗe kayar ki, sai ki samu Chikui, Kina Dangwala da shi kina ci.

Insha Allah Zaki sha Mamaki.

Ma’anar Chikui, Wani Nau’i ne na dabino Wanda ba’a fiye noma shi aƙasar Hausa ba, Amma baya wahala a kasuwa, shi ɗin Zaki Ganshi yanuna sosai kamar anzuba masa Zuma tsabar Laushin sa da zaƙin sa, kuma Manya-manya ne.

Related Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

© 2024 Mikiya - WordPress Theme by WPEnjoy
Danna Nan Ka Kalli Bidiyon 👈
error: Content is protected !!