Masha’Allah; Mawaki Aminu Alan Waka ya Aurar da ‘Yayansa Uku Mata, Allah Ya basu Zaman Lafiya

Masha’Allah; Mawaki Aminu Alan Waka ya Aurar da ‘Yayansa Uku Mata, Allah Ya basu Zaman Lafiya

A KARON farko, fitaccen mawaƙi, Sarkin Ɗiyan Gobir, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), ya yi bikin auren ‘ya’yan sa mata su uku a lokaci guda.

A ranar Lahadi da ta gabata, 28 ga Yuli, 2024, ne aka yi taron ɗaurin auren a gidan sa da ke unguwar Maidile cikin birnin Kano.

Taron ɗaurin auren ya samu halartar ɗimbin jama’a daga ciki da wajen ƙasar nan kama daga sarakuna, malamai, attajirai da manyan ma’aikatan gwamnati.

Ɗaurin auren dai na ‘ya’yan Ala ne guda uku waɗanda su ne manyan ‘ya’yan sa, wato Fatima, Aisha, da Bilkisu.

Shugaban Majalisar Malamai ta Arewa da kuma Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, yan a ɗaya daga cikin manyan malaman da suka jagoranci taron ɗaurin auren.

A ranar Juma’a, 26 ga Yuli aka shirya bikin Ranar Ƙauyawa, yayin da kuma a ranar Asabar aka yi taron yinin biki duk dai a gidan Ala da ke Maidile.

Taro mafi ƙayatarwa da aka shirya shi ne taron da aka yi a daren ranar ɗaurin auren, inda aka shirya liyafar cin abinci a babban ɗakin taro na Meenah Events Centre da ke unguwar Nassarawa G.R.A tun daga misalin ƙarfe 8 na dare har zuwa 12 na dare.

A wajen taron an gayyaci duk wani makusanci da aboki domin nuna ƙauna da kuma kara ga Ala. An yi shagalin biki, an ci abinci, an yi nishaɗi a wajen har zuwa lokacin da aka tashi daga taron. Allah ya sanya albarka a cikin auren, ya ba da zaman lafiya, amin.

Hotunan Gurin Daurin Aure

Related Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

© 2024 Mikiya - WordPress Theme by WPEnjoy
Danna Nan Ka Kalli Bidiyon 👈