Hotuna da Bayanin Mata Shida 6 da Jarumi Adam Zango Ya taba Aura a rayuwar shi.
Jarumi Adam A Zango fitaccen jarumi ne kuma mawaki a masana’antar Kannywood wanda ya dade yana taka rawar gani wajen shekara 20 a masana’antar.
Jarumin ya hadu da wata kaddara ta auri saki wanda idan ya Auri mace sai ya sake ta mutane suna ta zagin sa, Sai a satin nan jarumi Adam a Zango Ya fito ya bayyana laifin da yake kama Matansa dashi yake sakin su.
GA JERIN MATAN DA JARUMI ADAM A ZANGO YA TABA AURA.
1- Amina Rani
Amina Rani ita ce matar Adam A Zango ta farko da aura ya saka, Sunan da yaro guda 1 babban Dan Gidan Adam A Zango mai suna Aliyu (Haidar) ana Kiran ta da Maman Haidar yanzu.
2- Aisha
Aisha ita ce matar Adam A Zango ta biyu daya aura ya sake ta, ita ma suna da ‘ya ‘ya 3 a tsakanin su da Adam A Zango.
Aisha ta kasance yar Garin Zaria ce.
3- Maryam
Maryam ita ce matar Adam A Zango ta 3 da ya sake ta wace ya auro ta daga jihar Nassarawa, Kuma basu da ‘ya ‘ya a tsakanin su.
4- Maryam Ab Yola
Maryam Ab Yola ita ce matar Adam Zango ta 4 da ya aura kuma ya sake ta, Ya auri Maryam ne bayan sunyi wani film da ita mai suna NAS.
5- Ummul Khulsum
Ummi Khulsum ita ce matar Adam A Zango ta 5 wace ya sure ta a shekarar 2015 ‘yar kasar Cameroon, ya sake ta bayan ya aure ta suna da d’a daya a tsakanin su.
6- Safiya Challawa
Safiya Challawa Iya ce matar Adam A Zango ta 6 da ya aura a shekarar 2019 yar Kebbi state, Ya sake ta ita ma bayan ya aure ta suna da ‘ya guda daya a tsakanin su mai suna (DIANA)
Hoton Safiya Challawa