Innalillahi wa’innalaihi raji’un: Lafiya-lafiya an dauki azumi da ita ashe ba za ayi buɗe baki da ita ba, ta rasu yanzu…
Wannan budurwa sunan ta Fadimatu Lawal da ita aka dauki azumi yau bayan an gama murnar ganin watan Ramadan, ta tashi da azumi a bakinta kuma tana cikin ƙoshin lafiya har ma ta sanya “Status” na “Barka da azumin ranar farko wato Ramadan Day 1” amma Allah bai nufa za ayi buɗe baki da ita ba, ta rasu yanzu.
Ga Hotunan Status Din Da Tayi Yanzu.
Wani dan’uwanta ya shaidawa Mikiya cewa rashin lafiyar lokaci daya ya same ta, jikinta ya rikice dazu aka kaita asibiti a Unguwar Rimi Kaduna amma kan kace kwabo rai yayi halinsa ta rasu…