Shamsu Ɗan’iya: Babbar nasara ta a rayuwa ita ce rabuwa lafiya da mahaifiya ta.

Shamsu Ɗan’iya: Babbar nasara ta a rayuwa ita ce rabuwa lafiya da mahaifiya ta.

Matashin jarumin kannywood Shamsu Dan’iya ya bayyana halin da ya shiga na rashin Mahaifiyar sa, Hajiya Maimuna Yaya da ta rasu ranar Alhamis.

Shamsu Dan’iya yace ” Alhamdulilah abin da zan fara cewa shine dama su iyaye idan suka haife ka, burin su ka kyautata musu a lokacin da suke raye, sannan idan sun mutu kayi musu addu’a, wannan shine babbar nasarar da nayi na rashin Mahaifiya ta.

Da yake bayani kan irin yanayin da ya tsinci kanshi a lokacin da yake samun labarin mutuwar, ya ce, ” Ta dan dade tana jinya, ciwon ya dan ci karfin ta, Duk lokacin da aka kirani waya jira nake naji ance kaza nayi maza – maza nayi duba da yadda jikin nata yake bata iya magana sai dai tayi demostration.

“😭 Kirana da ta yi ina Kano tana ta ko karin tamin magana amma ta kasa, sai na kashe wayar na kira Yayana nace ya duba ya tambaya duk abin da take so amin Magana, wannan shine abun nayi da ita na karshe.

“Sannan gani na da ita na karshe shine, akwai wata tafiya da ta taso min zuwa kano zan gabatar da wasu harkokina na kasuwanci na, amma abu ne wanda bai shafi film ba aka kirani akace na zauna. Naje na same ta nace mata ‘Hajjiya, tafiya ta kamani, anyi min kiran gaggawa, amma insha Allah zan dawo, anyi min kirani akan harkar kasuwancina na daban.

“Sai tace babu damuwa, Allah ubangiji ya kani lafiya, tamin addo’i sosai, tace inje babu matsala. Wannan shine magana da ita na karshe 😭😭

Daga nan Shamsu Dan’iya ya yiwa abokan sana’ar sa godiya ta Musamman, Inda yace. ” Abukan sana’a ta ‘yan film a gurina sun zama’ yan uwa na uwa daya uba daya da su, Mazan su da Matansu babu wanda bai kirani ba yayi min ta’aziyyar Mahaifiya ta ba.

Related Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

© 2024 Mikiya - WordPress Theme by WPEnjoy
Danna Nan Ka Kalli Bidiyon 👈