INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI’UN. Kamal daya ne daga cikin mutanen da suka daukeni tamkar ciki daya muke,
INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI’UN. Kamal daya ne daga cikin mutanen da suka daukeni tamkar ciki daya muke,
Allah Ya Yìwa Jarumín Barkwancín Nàn Kamal Aboki Rasuwa Sakamakon Hatsarin Móta A Hanyar Dawowar Sú Daga Bornó Zúwa Jìhar Kanó.
Allah Ya Jiƙansa, Ya Gàfarta Masà. Amìn
Kamal daya ne daga cikin mutanen da suka daukeni tamkar ciki daya muke, yana karbar shawarata yakan kirani ya gaidani, yazo inda nake, ya karbi shawarata, bana mantawa akwai lokacin da zai yi wani Film daya shafi neman ilimin al Qurani, nine nayiwa wannan Film suna da (MABUDIN ILMI), babban abinda yake burgeni dashi girmama mutane da fara’a…
Bazan manta wannan ranar ba, Kamal Aboki yace dani oga bari nayi maka hoto, zan ajiye tarihin nayi tafiya da kai zuwa Maiduguri, muna wasa da dariya nace kajika da zolaya sai kace kayi tafiya da wannan babban mutum, cikin hukuncin Allah ashe hoton ne zai zama tarihin ka a gurina, Allah yayi maka Rahma Kamal, domin Kamal ba dan barkwanci bane kawai, mutum ne mai hankali nutsuwa da girmama mutane, Allah ya sani bansan wani aibun Kamal da zan iya fada a duniya ba, wannan tasa dole muji zafin mutuwarsa, amma duk son da muke masa Allah yana masa wanda yafi namu, shi yasa ya kirashi zuwa gare shi.
Allah ya gafarta masa yasa aljanna makomarsa.