Kidinafas sun sako mahaifiyar Rarara bayan mako uku da sace ta, Sun saketa saboda………

Kidinafas sun sako mahaifiyar Rarara bayan mako uku da sace ta, Sun saketa saboda………

BARAYI masu garkuwa da mutane, wato kidinafas, sun sako Hajiya Halima Adamu, mahaifiyar shahararren mawakin siyasa Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu ( Rarara), Bayan ta shafe kusan mako uku a hannnun su.

Da safiyar yau Laraba, Rarara ya dora hoton a tare mahaifiyar tasa a Instagram, a kasan hoton kuma ya rubuta cewa ” Alhamdulilah!!! Alhamdulilah!!! Alhamdulilah!!! Cikin yarda da amincin Ubangiji mun samu dawowar Mama cikin Aminci.

“Ina matukar Godiya ga Ubangiji, Ina Godiya ga ‘yanuwa Abokan sana’ata, Ina Godiya ga masoyana na fadin duniya baki daya.

“Hakika ba ni da bakin godiya a gareku. Allah ya saka da alkhairi, ya bar zumunci.

“Allah ya ba da lada, Na gode, Na gode, Na gode da Kulawa.”

Sannan wata majiya ta fada mana cewa “Barayin sun zo ne a kasa ba tare da wata hayaniya ba, Domin kuwa ba suyi harbi ko daya ba kuma su ka gama komai cikin minti kalilan. Tsohuwar bata yi musu wata garda ma ba lokaci da suka zo suka ce t tashi su tafi.

” Duk da cewa baryin sun sami mutane a gidan amma iya ita kadai suk dauka suka tafi.

“Ba a yi kokarin sun samu wasu mutanene a dauke da bindigogi.

A washe garin ranar ne rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama mutum biyi da ake zargi su na da Hannu a wajen sace tsohuwar.

Related Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

© 2024 Mikiya - WordPress Theme by WPEnjoy
Danna Nan Ka Kalli Bidiyon 👈