Tofah! Wa Yafi Kudi Tsakanin Sarkin Waka Da Rarara?

Wata Uwa Ta Jefar da Jariri Sabuwar Haihuwa a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira

Hukumar kula da sansanin ‘yan gudun hijira da ke Uhogua, kusa da Benin, ta ce wata da ba a san ko wacece ba ta jefar da wani jariri dan kwanaki biyu a cikin al’ummar.

Ko’odinetan sansanin Fasto Solomon Folorunsho ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a ranar Juma’a.

Folorunsho ya ce an gano jaririn ne a cikin wani dan jeji dake sansanin ta kofar shiga sansanin a ranar Juma’ar da misalin karfe 11 na safe.

Ya ce jaririn, wanda a halin yanzu yana karkashin kulawar lafiya a cibiyar kula da lafiya ta sansanin, wanda aka jefar da shi dauke da wani rubutun takarda.

“Mun gano jaririn mai kimanin kwana daya ko biyu a cikin jejin da ke kofar shiga sansanin.

“An jefar da jaririn tare da wani rubutu wanda ya karanta ‘don Allah a taimake ni in kula da shi. Ba zan iya kula da shi ba, domin ba ni da komai, kuma ba na son in kashe shi, don haka abinda ka bayar shi ne naka don Allah.

Ko’odinetan ya ce an kai rahoton ci gaban ga hukumomin da abin ya shafa da kuma hukumomin tsaro a jihar kamar ma’aikatar mata da ‘yan sanda da kuma hukumar tsaro ta DSS.

A halin da ake ciki, Folorunsho ya yi kira ga iyayen yaron da su kasance masu kwarin gwiwa su fito, inda ya kara da cewa yaro na bukatar shayarwa .

Related Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

© 2024 Mikiya - WordPress Theme by WPEnjoy
Danna Nan Ka Kalli Bidiyon 👈