Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin tarayya na sane da cewa azumin watan Ramadan mai gabatowa zai zo da kalubale masu tsanani ga akasarin ‘yan Najeriya saboda sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bullo da su.
Ya ce manufofin tattalin arziki da ake ɓullo da su na zuwa da kalubale da matsaloli, wanda zai zama “mafi tsanani ga talakawa.”
Daily Nigerian ta ruwaito cewa,Shettima ya bayyana haka ne a yayin taron lacca karo na 29 na gabanin watan Ramadan da daliban jami’ar Legas suka shirya a Legas.