Maryam Malika Da Mijinta Gaskiyar Abinda Yayi Sanadiyar Mutuwar Aurenta
Anyi Hirar Ne Tsakanin Hadiza Gabon Da Bakuwarta Wato Maryam Muhammad Malika, Wanda Yanzun Ake Kira Da Mero, Maryam Malika Ta Bayyanawa Duniya Wasu Zarge Zarge Da Akeyi Akanta Inda Ta Qaryata Su.
Da Farko Dai Mai Gabatarwa (Hadiza Gabon) Ta Fara Da Tambayar Maryam Malikan Kan Yadda Ya Taga Masana’antar KannyWood Inda Take Kafin Ta Tafi Tayi Aure Da Kuma Yanda Ta Dawo Ta Tarar Da Industry, Sai Bakuwar (Maryam Malika) Ta Bayyana Cewa An Sami Banbance Da Daman Gaske Musanman Ma Yanda Yanzun Ake Da Kayan Aiki Masu Kyau Fiye Dana Baya. Ta Kara Da Cewa Hatta Yadda Ake Tsarawa Ya Banbanta Da Na Baya.
Sai Hadiza Gabon Din Ta Tambayeta Shin Ya Yanayin Daukakarta Kafin Ta Tafi Tayi Aure Da Kuma Dawowarta.??
Sai Maryam Din Ta Bayyana Cewa Alhamdulillah! Har Yanzun Tana Da Masoya Kamar Yadda Ta Sami Masoya A Baya Kafin Tayi Aure.
Inda Tace Da A Baya Iya Manya Magidanta Ne Kawai Su Santa, Amma Yanzun Kuma Har Qananan Yara Ma Duk Sun Santa, Don Ko Fita Tayi Zataji Anata Kiran Sunanta.
An Tambayi Maryam Din Shin Ko Me Yayi Sanadiyyar Mutuwar Auren Nata, Kuma Shin Tana Son Mijin Nata Har Yanzun.
Bugu Da Kari Hadiza Gabon Din Kara Da Tambayar Maryam Din Wai Shin Dagaske Ne Abin Da Ake Cewa A Kotu A Raba Auren Nata Da Mijinta, Sai Maryam Din Taki Bada Amsa Tace Abar Wannan Maganar Kawai.
Mai Gabatarwa (Hadiza Gabon) Ta Tambaye Maryam Din Shin Menene GasKiyar Fada Da Tayi Da Producers Na Masana’antar KannyWood Kafin Tafiyar Auren Nata, Maryam Din Ta Bayyana Hakan A Matsayin Rashin Fahimta Na Mutane,
Inda Tace Koma An Sami Matsalar, Dama Zo Mu Zauna Ne Zo Mu Saba, Kuma Harshe Da Hakorina Ai Na Samun Matsala Wani Lokaci.
Ana Yawan Cewa Yan KannyWood Sunayin Aure Daga Baya Kuma Su Kashe Auren Su Dawo Domin Suci Gaba Da Harkarsu Ta Shirya Fim. Shine Kema Kin Kashe Aurenki Ne Domin Ki Dawo Ki Daura Daga Inda Ki Tsaya. ???
Sai Maryam Ta Bayyana Cewa Ita Sam Bata Da Wannan Niyyar A Ranta, Kuma Bata Taba Wannan Tunanin Ba, Don Haka Tayi Aure Ne A Lokacin Da Allah Ya Kaddara Mata. Sannan Auren Ya Mutu Ne Saboda Haka Allah Ya Kaddara Mata.