Babbar kotun jihar Kano a arewacin Najeriya tayi umarni a kama mawaki Ado Isah Gwanja.
Haka kuma kotun ta haramta masa yin waka ko zuwa taron biki a jihar.
Hukuncin kotun ya biyo bayan karar da majalisar malamai ta jahar kano ta shigar tana kalubalantar Gwanja da wasu mutane akan kalaman da sukeyi a wakoki.
Tuni dai Ado Gwanja ya garzaya gaban Babbar kotun jahar Kano inda ya nemi kotun ta bashi kariya wajan hana kamashi, inda a zaman kotun na yau tayi umarnin da aka kamashi tare da hanashi yin wakoki da kuma zuwa gidan biki har zuwa lokacin da zaβa kammala bincike.
Menene ra’ayinku akan wannan hukunci?